Shugaban Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) na ƙasa, Sanata David Mark, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakin gaggawa domin kawo ƙarshen kashe-kashe da garkuwa da mutane da ke ci gaba da faruwa a jihohin Benue da Filato.
A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Kola Ologbondiyan, ya fitar, David Mark ya yi Allah wadai da rahotannin kashe kusan mutum 16 a Otukpo da ke Jihar Benue da kuma wasu mutum tara a Ƙaramar Hukumar Riyom ta Jihar Filato.
Ya kuma nuna damuwa kan sace fasinjojin wata motar Benue Links da aka yi a kan hanyar Otukpo–Taraku–Makurdi, inda aka ce ‘yan bindiga sun yi awon gaba da dukkan fasinjojin motar.
David Mark ya bayyana hare-haren a matsayin “abin takaici kuma abin Allah wadai”, yana mai cewa ci gaba da kashe mutane da garkuwa da su na barazana ga tsaro da zaman lafiyar ƙasa.
Ya yi kira ga Rundunar Sojoji, Rundunar ‘Yan Sanda, Hukumar DSS da sauran hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen tattara bayanan sirri, sanya ido a yankunan da ke cikin haɗari da kuma tura ƙarin jami’an tsaro zuwa wuraren da ake fama da hare-hare.
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan ya kuma buƙaci a fara aikin ceto fasinjojin motar Benue Links cikin gaggawa, tare da kamo da hukunta masu hannu a kashe-kashen da garkuwa da mutanen.
David Mark ya jaddada cewa babu wata al’umma da ya kamata a bari cikin hannun masu aikata laifuka, yana mai cewa kare rayuka da dukiyoyin jama’a babban nauyi ne da kundin tsarin mulki ya ɗora wa gwamnati.
A ƙarshe, ya miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu, ya yi addu’ar samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata, tare da fatan a kuɓutar da mutanen da aka sace cikin ƙoshin lafiya.
Hare-haren na baya-bayan nan sun sake ƙara matsin lamba kan Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro domin ƙarfafa matakan kare rayuka, tabbatar da tsaro a manyan hanyoyi da kuma kawo ƙarshen hare-haren da ke ci gaba da addabar yankin Arewa ta Tsakiya.
