Uyo – Hukumar Kare Masu Ajiya a Bankuna ta Najeriya (NDIC) ta wayar da kan ɗaliban makarantar Federal Technical College da ke jihar Akwa Ibom kan muhimmancin ilimin harkokin kuɗi da kuma al’adar adana kuɗi, a wani shiri na bikin Financial Literacy Day 2026.
Jami’ar NDIC, Bowsan, ta bayyana cewa manufar shirin ita ce koya wa matasa kyawawan dabarun sarrafa kuɗi tun suna ƙanana, domin su zama manya masu iya tafiyar da harkokinsu cikin hikima a nan gaba.
Ta ce shirin na Bankers’ Committee ne, kuma yana ƙarfafa musamman ɗaliban makarantun sakandare su rungumi al’adar tanadi, samun ‘yancin cin gashin kai ta fuskar kuɗi, tare da kare kansu daga damfara ta kuɗi.
Shi ma Mai Kula da Yankin Port Harcourt na NDIC, Adefemi Shaba, ya ce an shirya taron ne domin taimaka wa ɗalibai su koyi yadda ake yanke shawara mai kyau kan harkokin kuɗi tun kafin su kai matakin jami’a.
Ya ƙara da cewa an kuma yi wa ɗaliban bayani kan ayyukan NDIC, da suka haɗa da kare kuɗaɗen masu ajiya, tabbatar da biyan diyya idan banki ya gaza, da kuma taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiyar tsarin kuɗi na ƙasa.
A nata ɓangaren, ɗaya daga cikin ɗaliban da suka halarci shirin, Udeme Effiong, ta gode wa NDIC bisa zaɓar makarantarsu, tana mai cewa shirin ya ƙara mata fahimta kan ilimin harkokin kuɗi kuma za ta iya wayar da kan wasu.
