Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Kasa (NERC) ta bayyana cewa ta mika ikon sa ido kan kasuwar wutar lantarki ga gwamnatocin jihohi 16, a wani mataki da ta ce zai bude sabon babi na gudanar da harkokin wutar lantarki a Najeriya.
Shugaban NERC, Dakta Musiliu Oseni, ya bayyana hakan yayin wani taron horaswa da aka shirya wa alkalan Babbar Kotun Jihar Legas domin kara fahimtarsu kan sauye-sauyen da ake yi a bangaren wutar lantarki.
Oseni ya ce taron na da nufin bai wa alkalai cikakken ilimi kan dokoki da bangarorin fasaha da suka shafi harkar wutar lantarki, domin su samu saukin yanke hukunci a shari’o’in da suka shafi wannan fanni.
Ya bayyana cewa bayan mika ikon kula da bangaren ga jihohi 16, ana sa ran za a rika fuskantar karin shari’o’i masu sarkakiya, don haka ya zama dole alkalai su fahimci yadda tsarin yake aiki.
NERC ta ce taron shi ne na farko cikin jerin shirye-shiryen da za a gudanar a sassa daban-daban na kasar domin inganta fahimtar bangaren shari’a kan dokoki da ka’idojin kasuwar wutar lantarki.
Hukumar ta kara da cewa za ta ci gaba da gudanar da irin wadannan tarurruka a sauran jihohin Najeriya domin tallafawa sauye-sauyen da ake yi a bangaren wutar lantarki da kuma tabbatar da cewa bangaren shari’a na tafiya tare da gyare-gyaren da ake aiwatarwa.
