Hanan Buhari, diyar marigayi tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ta bayyana cewa mahaifinta ya koya mata darajar gaskiya, juriya da kuma yi wa al’umma hidima ba tare da son kai ba, tana mai cewa tarbiyyarsa ta taka muhimmiyar rawa wajen gina rayuwarta.
Hanan ta bayyana haka ne a daren Alhamis a birnin Marrakech na kasar Morocco, bayan da ta karbi lambar yabo a matsayin daya daga cikin mutum 100 mafi fice da suka ba da gudunmawa wajen zaman lafiya a nahiyar Afirka, a taron Notable Africans Leadership and Business Summit.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Aikin taron, Kingsley Amafibe, ya fitar, Hanan ta sadaukar da lambar yabon ga marigayi mahaifinta tare da bayyana irin tasirin da ya yi a rayuwarta.
Ta ce, “Na sadaukar da wannan lambar yabo ga marigayi mahaifina, Shugaba Muhammadu Buhari, wanda tarbiyyarsa, ladabbinsa da kuma amincewar da ya yi da ni suka taimaka wajen gina ni zuwa matar da na zama a yau.”
Hanan ta kara da cewa Buhari ya koya mata muhimmancin gaskiya, juriya da hidimar al’umma ba tare da son kai ba, yana mai ba ta kwarin gwiwar yarda da kanta.
Ta yi alkawarin ci gaba da riko da kyawawan dabi’un da mahaifinta ya koyar da ita, musamman wajen karfafa mata da kuma bayar da gudunmawa mai amfani ga ci gaban al’umma.
A nasa bangaren, Kingsley Amafibe ya taya Hanan murnar samun wannan lambar yabo, yana mai bayyana ta a matsayin abin koyi da ke ci gaba da zaburar da matasa, musamman mata, su shiga harkokin shugabanci da ci gaban al’umma.
An gudanar da taron ne karkashin jagorancin gidauniyar DAVDAN Peace and Advocacy Foundation da kuma 100 Most Notable Peace Icons Africa, inda ya hada shugabannin siyasa, ‘yan kasuwa, masu tsara manufofi da jami’an diflomasiyya daga sassa daban-daban na Afirka domin karrama mutanen da suka ba da gagarumar gudunmawa wajen shugabanci, zaman lafiya, kasuwanci da ci gaba mai dorewa.
