Jami’an rundunar tsaro ta Agunechemba mallakar gwamnatin Jihar Anambra sun hallaka wasu ‘yan bindiga uku tare da tarwatsa maboyarsu a karamar hukumar Aguata bayan wani samame da suka kai tare da hadin gwiwar ‘yan sanda.
A yayin samamen da aka gudanar a daren ranar Talata, jami’an tsaron sun kuma kwato makamai masu hadari da suka hada da makamin roka (RPG), bindigogi kirar AK-47, da wata motar Hilux fara da kungiyar ke amfani da ita wajen ayyukan ta’addanci.
Mai magana da yawun Agunechemba, Nweke Nweke, ya bayyana a wata sanarwa cewa kungiyar ta dade tana haddasa rashin tsaro a jihar tare da aikata satar mutane, fashi da makami da sauran munanan laifuka.
Ya ce bayan tattara bayanan sirri, jami’an tsaro sun gano maboyar ‘yan bindigar a yankin Isuofia-Igboukwu, inda ake zargin suna tare da aikata fashi ga matafiya da sauran jama’a.
A cewarsa, da jami’an tsaro suka isa wurin, ‘yan bindigar sun yi kokarin tserewa tare da bude musu wuta, lamarin da ya janyo musayar wuta mai tsanani.
Sanarwar ta ce an hallaka mutum uku daga cikin ‘yan bindigar yayin da wasu da dama suka tsere da raunukan harbin bindiga.
Haka kuma, an bayyana cewa kungiyar ta kasance tana sanya kayan jami’an tsaron gwamnatin tarayya domin yaudarar jama’a da aikata laifuka.
Nweke ya kara da cewa wasu daga cikin mambobin kungiyar na da alaka da harin da aka kai wa tawagar shugaban ma’aikatan ofishin gwamnan Jihar Anambra, Ben Nwankwo, a farkon watan nan, wanda ya yi sanadin mutuwar jami’an ‘yan sanda biyu da fararen hula biyu.
Daga cikin kayayyakin da aka kwato akwai wasu laya-layai, jakunkuna da sauran abubuwan da ake zargin suna da alaka da ayyukan laifi.
Masu ruwa da tsaki a harkokin tsaro a jihar sun bayyana wannan nasara a matsayin wani babban ci gaba a yaki da matsalar garkuwa da mutane da ayyukan ta’addanci a Anambra.
Sun kuma tabbatar da cewa za a ci gaba da farautar sauran ‘yan kungiyar da suka tsere domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar.
