An dage fafatawar da ake sa ran za ta sake hada fitattun tsoffin zakarun damben duniya, Floyd Mayweather da Manny Pacquiao, ba tare da sanya sabuwar ranar da za a gudanar da ita ba.
Sanarwar dage fadan ta fito ne daga tawagar Manny Pacquiao a kasar Philippines bayan rahotanni sun bayyana cewa an dakatar da wani wasan baje koli da Mayweather zai yi a kasar Girka sakamakon rikicin shari’a da ya shafi masu shirya fafatawar.
Mayweather da Pacquiao sun fara samun sabani ne bayan Mayweather ya bayyana cewa fadan da aka sanar zai kasance wasan baje koli ne kawai, sabanin yadda tawagar Pacquiao ke ganin lamarin.
A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Juma’a, tawagar Pacquiao ta dora alhakin dage fadan kan matsalolin shari’a, cunkoson jadawalin shirye-shirye da kuma matsalolin kudi da suka shafi bangaren Mayweather.
Kamfanin shirya wasanni na CSI ya shigar da kara a kotu yana neman a biya shi akalla dala miliyan 4.65, yana mai cewa ya riga ya biya Mayweather kudin samun cikakken ikon shirya fafatawar da kuma wani wasan baje koli da Mike Tyson wanda bai samu ba.
Sanarwar ta ce idan aka warware matsalolin da ke tsakanin Mayweather da kamfanin CSI, za a iya sake tsara wasan baje koli tsakanin Mayweather da Mike Tyson, wanda ake sa ran zai gudana a watan Satumba.
Tawagar Pacquiao ta kuma bayyana cewa idan za a sake shirya fafatawar tsakaninsa da Mayweather, hakan ba zai yiwu ba sai a farkon shekarar 2027.
Mayweather, mai shekaru 49, ya yi ritaya daga damben ƙwararru a shekarar 2017 ba tare da ya taba shan kaye ba, inda ya kammala aikinsa da nasarori 50 ba tare da rashin nasara ko daya ba.
Fadan farko tsakanin Mayweather da Pacquiao a shekarar 2015 ya kasance daya daga cikin fafatawar damben da ta fi samar da kudaden shiga a tarihin wasan.
