Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Sagbama/Ekeremor ta Jihar Bayelsa, Hon. Fred Agbedi, ya zama sabon Jagoran ‘Yan Adawa (Minority Leader) na Majalisar Wakilai.
Agbedi, wanda ke cikin bangaren jam’iyyar PDP karkashin jagorancin Taminu Turaki, ya maye gurbin Hon. Kingsley Chinda bayan ya yi murabus daga mukamin tare da komawa jam’iyyar APC.
Chinda ya sauya sheka ne bayan lashe zaben fidda gwani na gwamnan jihar Rivers na jam’iyyar APC gabanin babban zaben shekarar 2027.
Haka kuma, dan majalisar mai wakiltar Darazo/Ganjuwa a Jihar Bauchi karkashin jam’iyyar APM, Hon. Manu Soro, ya zama Minority Whip, yayin da dan majalisar ADC daga Jihar Sokoto, Hon. Abdulsammad Dasuki, ya zama Mataimakin Jagoran ‘Yan Adawa.
An bayyana sabbin nade-naden ne cikin wata wasika daga ‘yan adawa a majalisar da Kakakin Majalisar Wakilai, Hon. Abbas Tajudeen, ya karanta a zaman majalisar na ranar Alhamis.
A cewar wasikar, an cimma matsaya kan sabbin shugabannin ne ta hanyar yarjejeniya tsakanin ‘yan adawar majalisar.
Wannan ci gaba ya kawo karshen takaddamar da ta dauki makonni ana yi kan wanda zai jagoranci ‘yan adawa bayan kusan ‘yan majalisa 60 daga cikin 80 suka mara wa Hon. Ikenga Ugochinyere baya domin zama Minority Leader.
Sai dai a ranar Laraba, Majalisar Wakilai ta yi gyara ga dokokinta, inda ta haramta wa sabbin ‘yan majalisa masu wa’adi na farko rike mukaman shugabanci a majalisar.
Bayan wannan sauyi, Ugochinyere ya janye takararsa ta neman zama Jagoran ‘Yan Adawa, yana mai cewa ya yi hakan ne domin girmama sabbin dokokin majalisar da kuma tabbatar da hadin kan bangaren ‘yan adawa.
Ya jaddada cewa kungiyar ‘yan adawa za ta ci gaba da aiki tare domin kare dimokuradiyya da kuma tabbatar da zaman lafiya a majalisar.
