Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Lagos ta karyata rahotannin da ke yawo cewa wasu ‘yan bindiga na shirin kai hari tare da sace dalibai a makarantu, tana mai cewa babu wani sahihin bayanan sirri da ke nuna akwai irin wannan barazana a jihar.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Benjamin Hundeyin, ya wallafa a shafinsa na X ranar Litinin, rundunar ta ce ta samu labarin wata sanarwa da ake yadawa da aka ce an manna a wata makaranta, amma ta bukaci iyaye, masu kula da yara, shugabannin makarantu da mazauna jihar da su kwantar da hankalinsu.
Rundunar ta bayyana cewa a halin yanzu babu wata kwakkwarar hujja ko bayanan sirri da ke nuna cewa akwai shirin kai hari ga makarantu a jihar Lagos.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Lagos, CP Olohundare Jimoh, ya bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa tare da kara tsaurara matakan tsaro a makarantu da sauran muhimman wurare a fadin jihar.
Haka kuma, rundunar ta ce jami’anta tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro sun bazama domin kare makarantu, muhimman kayayyakin gwamnati da kuma al’ummomi daban-daban.
“Babu wani sahihin bayanin sirri da ke nuna akwai wata barazana ta kai hari a makarantu ko wasu wurare a Lagos. Muna rokon jama’a da su guji firgita ko yada jita-jita,” in ji sanarwar.
Rundunar ta kuma jaddada cewa ba za ta lamunci duk wani yunkuri daga masu laifi da ke neman tayar da hankalin jama’a ko kawo cikas ga zaman lafiya ba.
“Duk wanda aka samu yana yada tsoro ko aikata wani abu da zai haddasa rashin tsaro za a dauki matakin doka a kansa,” rundunar ta bayyana.
An kuma bukaci mazauna jihar su kasance masu sa ido tare da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai kan duk wani abu da ya tayar musu da hankali.
