Dan wasan gaba na Super Eagles, Paul Onuachu, ya bayyana cewa Najeriya na da isasshen ƙarfi da hazaka da za ta iya fafatawa tare da doke kowace ƙasa a duniya, duk da cewa ta kasa samun tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA ta 2026.
Onuachu ya bayyana hakan ne gabanin wasan sada zumunci da Super Eagles za ta buga da Poland a birnin Warsaw ranar Alhamis.
Haka kuma, Najeriya za ta kara da Portugal a wani wasan sada zumunci mai muhimmanci a mako mai zuwa, yayin da mai horar da ƙungiyar, Eric Chelle, ke ci gaba da shirye-shiryen manyan gasa na gaba.
Super Eagles na shiga waɗannan wasanni cikin kwarin gwiwa bayan kare kambunta na Unity Cup da ta yi a karshen makon da ya gabata, abin da ya nuna irin ci gaban da ƙungiyar ke samu ƙarƙashin jagorancin Chelle.
Onuachu ya ce ƙungiyar na da manyan ‘yan wasa masu inganci da za su iya kalubalantar kowace babbar ƙasa a fagen ƙwallon ƙafa.
“Muna da ƙwararrun ‘yan wasa da za su iya taka leda da kowace ƙasa a duniya, kuma muna fatan nuna hakan a wasannin da za mu buga da Poland da Portugal,” in ji Onuachu.
Sai dai ya amince cewa rashin samun gurbin shiga gasar cin kofin duniya ya kasance babban abin takaici ga ‘yan wasa da magoya baya.
“Abin takaici ne cewa ba za mu halarci gasar kofin duniya ba, duk da cewa muna da ‘yan wasa masu matakin duniya. Amma wannan shi ne ƙwallon ƙafa,” ya ƙara da cewa.
Rashin samun tikitin shiga gasar ta 2026 ya kasance babban koma baya ga Najeriya, amma wasannin baya-bayan nan sun nuna alamun cewa ƙungiyar na tafiya a hanya mai kyau.
Ana sa ran wasannin sada zumunci da Poland da Portugal za su bai wa Eric Chelle damar gwada ƙarfinsa da tantance ‘yan wasa gabanin manyan gasa masu zuwa, tare da ci gaba da gina ƙungiya mai ƙarfi da za ta dawo da martabar ƙwallon ƙafar Najeriya a duniya.
