Kotun Coroner da ke Igbosere a Lagos Island ta dakatar da ci gaba da sauraron shari’ar bincike kan mutuwar Nkanu Adichie-Esege, ɗan watanni 21 na marubuciya Chimamanda Ngozi Adichie da Dr. Ivara Esege, har sai an samu umarni daga Babban Coroner na jihar, Justice Mojisola Dada.
An dakatar da zaman ne bayan lauyan Gwamnatin Jihar Lagos ya shaida wa kotu cewa Babban Lauyan Gwamnati (Attorney-General), Lawal Pedro, ya ba da umarnin a dakatar da shari’ar har sai bayan wani taro da za a yi tsakanin dukkan bangarorin a ranar 12 ga Mayu, 2026.
Sai dai Mai Shari’a Atinuke Adetunji ta nuna rashin amincewa da wannan umarni, tana mai cewa kotu tana da ‘yanci kuma ba ta ƙarƙashin ma’aikatar shari’a kai tsaye.
Ta ce: “Ina ganin abin takaici ne cewa Attorney-General zai ɗauki irin wannan mataki ba tare da sanar da kotu ba. Ba shi da ikon umartar kotu, bisa tsarin raba iko tsakanin hukumomi.”
Lauyan iyayen marigayin, Adeyinka Aderemi (SAN), ya ce tun da farko an sanar da bangarori taron da za a yi a ranar Talata, amma daga baya aka sauya shi ba tare da cikakken sanarwa ba sai a daren Litinin.
Ya kuma tabbatar da cewa mahaifin yaron yana cikin kotu kuma a shirye yake ya bayar da shaida.
Wannan bincike ya fara ne a ranar 25 ga Fabrairu, inda ake binciken yadda Nkanu ya rasu bayan an tura shi daga Asibitin Atlantis Paediatric zuwa Euracare Multi-Specialist Hospital domin wasu jinya.
Rahotanni sun ce yaron ya rasu ne da safiyar 7 ga Janairu, 2026, yayin da ake shirin tura shi zuwa Johns Hopkins Hospital don ƙarin kulawa.
