Kamfanin Benid Industries Limited tare da haɗin gwiwar Sanity Multi-Efforts Limited (SMEL) sun fara wani shiri na neman bayyanannun umarni kan harajin da ya dace a bi a hanyoyin Najeriya, tare da nufin kawo ƙarshen haramtattun karɓar kuɗi da cin zarafin direbobi a manyan hanyoyi.
A cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a Lokoja, Shugaban Kamfanin Benid Industries, Dr. Idoko Bartholomew Chukwuma, ya bayyana cewa wannan mataki an ɗauke shi ne a matsayin martani ga sabuwar manufar gyaran haraji ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta shekarun 2025–2026.
Dr. Idoko ya bayyana damuwa kan yadda direbobin ababen hawa ke fuskantar matsin lamba da cin zarafi daga wasu da ba su da hurumin karɓar haraji, inda ake kafa shingayen hanya ba bisa ƙa’ida ba domin karɓar kuɗi.
Ya ce wannan hali yana rage kuɗaɗen shiga na jihohi na gaskiya tare da karya dokokin haɗin gwiwar hukumar haraji da aka amince da su a Disamba 2025.
A cewarsa, wannan haɗin gwiwa da aka kafa tare da goyon bayan coci-coci, masana’antu, ƙungiyoyin sufuri da masu motoci a faɗin ƙasa, ya haifar da aika wasiƙu zuwa dukkanin hukumomin haraji na jihohi 36 da Abuja ta hannun SMEL, ƙarƙashin jagorancin Prince Dan Olaitan Dada.
Dr. Idoko ya jaddada cewa shirin ba na adawa ba ne, illa kawai na neman tattaunawa da fahimtar juna.
Ya ce:
“Muna neman gaskiya ne kawai. Jihohi su bayyana harajin da doka ta amince da shi, hanyoyin biyan kuɗi, da kuma hujjar doka ga kowanne nau’in haraji. Idan aka yi haka, kowa zai bi doka.”
Ya kara da cewa fayyace tsarin haraji zai kare direbobi, ya ƙara inganta kudaden shiga na jihohi (IGR), tare da taimakawa wajen aiwatar da tsarin tattalin arziki na zamani mai sauƙin kasuwanci.
Haka kuma, ya koka kan yadda yawan haraji da karɓar kuɗi ba bisa ƙa’ida ba ke jawo asarar miliyoyin naira ga ‘yan kasuwa a kowane wata.
A matakin wucin gadi, kamfanin ya umarci direbobi da su guji rikici, su ƙi biyan kuɗi ga wadanda ba su da takardun hukuma, su bi hanyoyin biyan kuɗi na gwamnati, sannan su kai rahoton duk wani cin zarafi ga hukumomin tsaro.
Dr. Idoko ya ce wannan mataki yana da nufin tsaftace harkokin sufuri a Najeriya cikin bin doka da oda.
Ya ƙare da cewa wannan shiri na daga cikin ƙoƙarin farko na ɓangaren masu zaman kansu wajen tallafawa aiwatar da gyaran haraji na shugaban ƙasa a fadin
