Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN), ya nuna goyon baya ga wata shari’a da ke neman a soke rijistar wasu jam’iyyun siyasa a Najeriya, ciki har da jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), bisa zargin karya dokar kundin tsarin mulki.
Wannan na kunshe ne cikin wata takardar shari’a da aka shigar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a shari’a mai lamba FHC/ABJ/CS/2637/2026.
A cikin karar, an sanya Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC), Babban Lauyan Gwamnati, ADC, Action Alliance, Action Peoples Party, Accord da Zenith Labour Party a matsayin wadanda ake kara.
A cewar takardar da aka shigar karkashin Dokar Kotun Tarayya ta 2019, AGF ya bayyana cewa ya amince da karar da aka shigar “gwargwadon nauyin da kundin tsarin mulki ya dora masa.”
AGF ya ce aikinsa ne kare kundin tsarin mulkin Najeriya, tare da tabbatar da bin doka da oda a dukkan matakai na gwamnati da zabe.
Ya kara da cewa yana da alhakin tallafawa duk wani mataki da ke tabbatar da aiwatar da dokoki da kare tsarin dimokuradiyya a kasar.
Takardar ta kuma bayyana cewa AGF yana da nauyin yin aiki tare da hukumomin gwamnati da jama’a domin tabbatar da bin doka da inganta adalci.
Haka kuma, AGF ya bayyana cewa karamin karfi da wasu ‘yan kasa ke da shi na daukar matakin shari’a ne ya sa dole a tallafa wa irin wadannan shari’o’i domin kare hakkin jama’a.
A cewar takardar, akwai bukatar tabbatar da cewa duk jam’iyyar siyasa da ke shiga zabe ta cika sharuddan da kundin tsarin mulki ya gindaya, musamman karkashin sashe na 225A.
AGF ya kuma gargadi cewa ci gaba da wanzuwar jam’iyyun da ba sa aiki yadda ya kamata na iya haddasa cunkoso a katin zabe, da kara kashe kudin gwamnati, da kuma dagula tsarin gudanar da zabe.
Ya kara da cewa gazawar INEC wajen daukar matakin cire rajistar irin wadannan jam’iyyun na iya zama karya doka da za a iya kalubalanta a kotu.
Wannan shari’a na daga cikin sabbin muhawara kan ikon INEC da kuma yadda ake tafiyar da tsarin jam’iyyun siyasa a Najeriya.
