Tsohon ɗan Majalisar Wakilai, Omoregie Ogbeide-Ihama, ya shiga takarar kujerar Sanatan Edo Kudu a ƙarƙashin jam’iyyar APC domin zaɓen 2027.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya yi jawabi a Ward II da ke Oredo Local Government Area na Jihar Edo, inda ya ce gogewarsa ta shekara takwas a Majalisar Tarayya ta sa shi ya fi dacewa da kujerar.
Ogbeide-Ihama ya ce zaɓen 2027 zai buƙaci ƙwarewa, iya aiki da kuma karɓuwa a matakin ƙasa, ba wai son rai ko siyasar ƙungiya kaɗai ba.
Ya ce:
“Na shafe shekaru takwas a Majalisar Wakilai. Dokoki da tsarin aiki na majalisun biyu iri ɗaya ne, don haka ni ne mafi ƙwarewa a cikinsu.”
Ya ƙara da cewa majalisar dattawa tana buƙatar mutum mai kwarewa, domin gudanar da muhimman dokoki da kuma kawo ci gaban mazabu.
Tsohon ɗan majalisar ya kuma ce ya taɓa kawo ayyukan tarayya a mazabarsa, yana mai cewa yana da tarihin nasarar zaɓe ko da yana cikin adawa.
“Na ci zaɓe a lokutan da nake cikin adawa, na kuma lashe ward 12-12 a jere,” in ji shi.
Ogbeide-Ihama ya jaddada cewa yana da alaƙa mai ƙarfi da talakawa, inda ya bayyana kansa a matsayin ɗan takara da ke da gogewa da kuma wakiltar sabuwar ƙarni.
Ya kuma karyata zargin cewa ba cikakken ɗan APC ba ne, yana mai cewa yana da cikakken zama a jam’iyyar.
A nasa jawabin, ya ce tallafi daga kowane bangare a siyasa abu ne da aka saba da shi, ba abin zargi ba ne.
Ya kuma roƙi ‘yan jam’iyyar APC a Edo Kudu da su guji rarrabuwar kai, su mayar da hankali wajen zaɓar ɗan takara mafi cancanta domin cin zaɓe a 2027.
Ogbeide-Ihama ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa APC za ta yi nasara a zaɓen gaba idan ta tsaya kan cancanta da karɓuwa.
