Cibiyar Centre for Democracy and Development (CDD-West Africa) ta bayyana damuwa kan tsadar kudin fom da jam’iyyar APC ta kafa, tana mai cewa hakan na iya mayar da harkokin siyasa ga masu kudi kawai.
/ CIKAKKEN LABARI
Jam’iyyar APC ta fitar da jadawalin shirinta na zaben 2027, inda ta sanya kudin neman takarar mukamai daban-daban a matakai masu tsada.
A cewar jadawalin:
Shugaban kasa:
Fom na sha’awa: ₦30m
Fom na takara: ₦70m
Gwamna:
Sha’awa: ₦10m
Takara: ₦40m
Sanata:
Sha’awa: ₦3m
Takara: ₦17m
Majalisar Wakilai:
Sha’awa: ₦1m
Takara: ₦9m
Majalisar Jiha:
Sha’awa: ₦1m
Takara: ₦5m
MARTANI DAGA CDD-WEST AFRICA
Shugaban cibiyar, Dr. Gauda Garuba, ya ce wannan mataki na APC na iya kara yawan cin hanci da rashawa a siyasar Najeriya.
Ya bayyana cewa ‘yan takara da suka kashe makudan kudi wajen neman mukami za su iya mayar da hankali kan dawo da kudin da suka kashe, maimakon hidima ga jama’a.
“Wannan mataki yana mayar da siyasa ga masu kudi kawai,” in ji shi.
SUKAR TSARIN DEMOKRADIYYA
CDD ta ce wannan tsarin na APC na iya tauye ‘yancin dimokuradiyya, musamman ga matasa da mata.
Ta ce hakan na sabawa kokarin da aka dade ana yi na:
“Not Too Young to Run”
da kuma kudirin kara wakilcin mata a siyasa
HATSARI GA MULKI
Garuba ya kara da cewa irin wannan tsari na iya haifar da matsala a mulki, domin wadanda suka kashe kudi a siyasa za su iya fifita dawo da kudinsu fiye da yi wa jama’a aiki.
