Matasa mambobin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) na shirin gudanar da zanga-zanga a jihohin Lagos, Ogun da Jigawa a yau, domin ƙara matsin lamba ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) a cikin rikicin shugabanci da ke kara ta’azzara a jam’iyyar.
Zanga-zangar, wacce ake gudanarwa karkashin hashtag #AmupitanMustGo, za ta gudana a ofisoshin INEC da ke wadannan jihohi uku. Masu shirya ta sun bayyana cewa wannan mataki ne na neman a bi doka da oda da kuma tabbatar da gaskiya da adalci.
Shugaban matasan ADC na ƙasa, Balarabe Rufai, ne ya bayyana shirin a shafinsa na X (tsohon Twitter) a ranar Litinin, inda ya kuma wallafa fastoci da ke nuna taken zanga-zangar mai suna “Operation Occupy INEC”.
A cewar Rufai, zanga-zangar a Lagos za ta fara ne da karfe 8 na safe a Yaba College of Technology, yayin da ta Ogun za ta gudana da karfe 11 na safe a ofishin kamfanin NNPC da ke Abeokuta. Sai dai ba a bayyana cikakken wurin gudanar da zanga-zanga a Jigawa ba har zuwa lokacin rubuta wannan rahoto.
Wannan mataki na zuwa ne bayan wata zanga-zanga da matasan ADC suka gudanar a ofishin INEC da ke Lagos, inda suka rika rike alluna suna neman shugaban hukumar, Joash Amupitan, ya yi murabus tare da dawo da shugabancin jam’iyyar karkashin David Mark.
Rufai ya bayyana cewa zanga-zangar tana da nufin tabbatar da dimokuraɗiyya ta hanyar lumana da bin doka.
