Shugaban kuma Wanda ya kafa Omega Power Ministries (OPM), Apostle Chibuzor Gift Chinyere, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta soke jarabawar shiga jami’a ta UTME da Hukumar JAMB ke shirya wa, yana mai cewa tsarin jarabawar ya daina dacewa da zamani kuma yana wahalar da dalibai.
Apostle Chinyere ya yi wannan kira ne a ranar Lahadi yayin wa’azi da ya gabatar a babban hedikwatar cocin da ke Fatakwal, Jihar Rivers, inda ya ce yawan matakan da dalibi ke bi kafin samun shiga jami’a ya zama abin gajiya da damuwa.
Ya bayyana cewa dalibi a Najeriya zai fara da WAEC, sannan JAMB, daga bisani post-UTME, kafin a duba maki na kofa (cut-off mark) na jami’a da na sashen karatu. Ya ce idan bai cika sharuddan ba, sai ya sake shekara guda yana maimaita jarabawa.
“Wannan tsarin yana matukar wahalar da matasa,” in ji shi.
Ya kara da cewa JAMB ta riga ta wuce aikinta na farko, ganin cewa jami’o’i har yanzu suna sake yin tantancewa bayan UTME.
- Ya bukaci gwamnati ta duba tsarin domin saukaka wa dalibai shiga manyan makarantu a Najeriya.
