Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, na gudanar da manyan ayyukan gyaran hanya da magance ambaliya a sassa daban-daban na birnin Benin, kuma yawancin ayyukan sun kusa kammala.
Daya daga cikin manyan ayyukan shi ne hanyar Amufi–Okpagha–Egan mai tsawon kilomita 8.25, wadda ke da matsalar ambaliya da zaizayar ƙasa na tsawon shekaru.
Masu aikin injiniya sun ce an kai kusan kashi 80 cikin 100 na aikin magudanan ruwa, kuma ana sa ran kammala aikin a watan Mayu 2026.
Haka kuma a Ramat Park, aikin gadar sama ya kusa kammaluwa inda ya kai sama da kashi 90 cikin 100, tare da magudanan ruwa don rage cunkoso da ambaliya.
A wasu yankuna kamar Evbhukhu da Old Sapele Road, ana ci gaba da gyaran hanyoyi da gina magudanan ruwa domin hana lalacewar hanya da ambaliya.
Mutanen yankin sun ce suna ganin sauƙi a halin da ake ciki, domin ayyukan suna taimakawa wajen sauƙaƙa zirga-zirga da harkokin kasuwanci.
- Gwamnati na ci gaba da haɗa gina hanyoyi da magudanan ruwa domin magance matsalar ambaliya gaba hi ɗaya.
