‘Yan majalisar wakilai na jam’iyyar Democrat a Amurka sun gabatar da kudurin tsige Sakataren Tsaro, Pete Hegseth, bisa zargin aikata “manyan laifukan ofis” (high crimes and misdemeanors).
Rahotanni sun bayyana cewa an zarge shi da kaddamar da hare-haren soja kan Iran ba tare da amincewar Majalisa ba, abin da ke keta ikon da Kundin Tsarin Mulkin Amurka ya ba Majalisa na ayyana yaki.
Wannan mataki ya fito ne daga ‘yar majalisa Yassamin Ansari, wadda ta wallafa sanarwar a shafin X (Twitter), inda ta ce Hegseth ya jefa sojojin Amurka cikin hadari da kuma keta dokar yaki.
Kudurin ya kuma zarge shi da rashin bin dokokin yakin duniya, ciki har da rahoton harin da ya shafi makaranta a Minab, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 170, ciki har da yara da malamai — duk da cewa ana ci gaba da bincike kan sahihancin wannan rahoto.
Haka kuma, ‘yan Democrat sun zarge shi da amfani da dabarun soja da ake kira “double tap strikes” kan jiragen da ake zargin safarar miyagun kwayoyi a Caribbean, tare da zargin yin sakaci da bayanan sirri na soja.
Sai dai kakakin Pentagon, Kingsley Wilson, ya yi watsi da wannan yunkuri, yana mai cewa matakin siyasa ne kawai na ‘yan Democrat domin jawo hankalin jama’a.
Yunkurin tsige shi na zuwa ne a daidai lokacin da rikici ke kara tsananta a Gabas ta Tsakiya, lamarin da ya taimaka wajen tashin farashin mai a duniya.
