Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa kuma Shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan, ya bukaci a gudanar da bincike mai gaskiya kuma mai zaman kansa kan harin sama da ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 50 a yankin kan iyakar Borno da Yobe a ranar Asabar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a kalla mutane 56, mafi yawansu ’yan kasuwa, suka rasa rayukansu yayin da wasu 14 suka jikkata a harin da aka kai a Kasuwar Jilli, wadda ke tsakanin Kananan Hukumomin Gubio a Jihar Borno da Geidam a Jihar Yobe.
Rahotanni sun bayyana cewa ana zargin an kai harin ne ne a yayin wani farmaki na soja da ake kaiwa kan mayakan Boko Haram da ake zargi.
Sai dai har yanzu hukumomin soja ba su fitar da cikakken bayani kan lamarin ba, yayin da al’umma ke ci gaba da nuna damuwa kan yadda fararen hula suka shiga cikin hatsarin.
Ahmad Lawan ya ce dole ne gwamnati ta tabbatar da an gudanar da bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru tare da hana aukuwar irin wannan iftila’i a nan gaba.
