Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa Amurka za ta fara aiwatar da wani mataki na katse zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigin Strait of Hormuz, bayan da rahotanni suka ce tattaunawa tsakanin bangarorin da ke rikici ta rushe a Pakistan.
A cikin sakon da ya wallafa a kafar sada zumunta a ranar Lahadi, Trump ya ce manufar matakin ita ce share nakiyoyi daga yankin tare da sake buɗe hanyar ruwa ga dukkan jiragen ruwa, amma ya jaddada cewa bai kamata Iran ta ci riba daga ikon da take da shi kan mashigin ba.
Ya ce:
“Nan take, Rundunar Sojin Ruwa ta Amurka, mafi ƙarfi a duniya, za ta fara aikin BLOCKADE na dukkan jiragen ruwa da ke shigowa ko fita daga Strait of Hormuz… Duk wani ɗan Iran da ya harbi mu ko jiragen ruwa masu zaman lafiya, za a hallaka shi.”
A wani bayani da aka danganta ga US Central Command (CENTCOM), an ce dakarunta za su fara aiwatar da matakin hana zirga-zirgar jiragen ruwa zuwa da daga tashoshin jiragen ruwa na Iran daga ranar 13 ga Afrilu, 1400 GMT.
CENTCOM, wacce ita ce United States Central Command, ta ce matakin zai shafi dukkan jiragen ruwa ba tare da bambanci ba, ciki har da jiragen ƙasashe daban-daban da ke shiga ko fita daga tashoshin Iran da yankunan gabar tekun Fasha da Tekun Oman.
Sai dai ta bayyana cewa ba za ta hana zirga-zirgar jiragen ruwa da ke wucewa zuwa tashoshin da ba na Iran ba a cikin Strait of Hormuz ba.
Haka kuma, ta ce za a fitar da ƙarin bayani ga masu jiragen ruwa ta hanyar sanarwar hukuma kafin fara aiwatar da matakin, tare da gargadin su su riƙa bin “Notice to Mariners” da kuma tuntuɓar rundunar sojin ruwa ta Amurka a tashar sadarwar teku (channel 16) yayin tafiya a yankin Tekun Oman da kusa da mashigin.
Mashigin Strait of Hormuz na ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin jigilar mai a duniya, kuma duk wani tangarda a yankin na iya shafar kasuwancin makamashi na duniya baki ɗaya.
