Matatar fetur ta Dangote ta sanar da rage farashin litar man fetur daga Naira 890 zuwa Naira 825. Hukumar gudanarwar matatar ta bayyana hakan a yau Laraba, tana mai cewa matakin na da nufin saukakawa ’yan Najeriya yayin da watan Azumin Ramadan ke karatowa.
Idan za a iya tunawa, a lokacin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara, matatar ta rage farashin man domin tallafa wa jama’a.
