Wanda ya kafa Sahara Group, Tonye Cole, ya bayyana cewa son da ake yi wa kamfanonin ƙasashen waje a Najeriya a lokacin da suka fara kasuwanci ya tilasta su yin rajistar kamfaninsu a ƙasashen waje domin samun amincewar kwastomomi.
Cole ya bayyana hakan ne yayin da yake tuna irin ƙalubalen da shi da abokan kasuwancinsa suka fuskanta a farkon tafiyarsu.
A cewarsa, a wancan lokaci mutane da dama sun fi yarda da kamfanonin baƙi fiye da na ‘yan Najeriya.
“Idan kai farar fata ne a Najeriya a lokacin, kusan komai zai yi maka sauƙi,” in ji shi.
Ya ce ƙalubalen bai tsaya kan kasancewarsu ‘yan Najeriya kaɗai ba, har ma da kasancewarsu matasa masu shekaru tsakanin 27 zuwa 28, lamarin da ya sa mutane ba su yarda cewa su ne suka mallaki kamfanin ba.
Saboda haka, suka yi rajistar Sahara Group a Isle of Man, tare da kafa reshe a Birtaniya domin ya ba kamfanin martaba a idanun masu hulɗa da su.
Cole ya kuma bayyana cewa sun haɗa kai da wani tsohon malaminsu, wanda ake kira Dr. J, suka riƙa nuna cewa suna aiki ne a ƙarƙashinsa a matsayin ma’aikata, ba su ne masu kamfanin ba.
A cewarsa, wannan dabara ta taimaka musu sosai wajen samun kwangiloli da amincewar kwastomomi, domin mutane sun fi yarda da kamfanin da suke ganin mallakin wani ɗan ƙasar waje ne.
Sai dai bayan kusan shekara uku, mutane suka fara tambayar dalilin da ya sa ba a taɓa ganin wannan Dr. J ba, wanda hakan ya sa suka daina amfani da wannan tsarin.
Cole ya ce wannan ƙwarewar ta nuna irin ƙalubalen da ‘yan kasuwar Najeriya ke fuskanta a lokacin wajen gina kasuwanci.
Ya ƙara da cewa tafiyarsa ta kasuwanci ta fara tun yana ɗalibin gine-gine a Jami’ar Legas (UNILAG), inda shi da abokansa suka fara yin ƙirar gine-gine ga kamfanoni kafin daga bisani su kafa Sahara Group, wanda yanzu ya zama babban kamfanin makamashi mai ayyuka a ƙasashe da dama na duniya
