Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Osun, Adewale Egbedun, ya bayyana cewa Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, Ibrahim Gotan, ne ya bayar da umarnin kama Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG), Teslim Igbalaye, saboda wani rikici da ya faru a wani taron masu ruwa da tsaki na hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC).
A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, Egbedun ya ce ya halarci taron tare da Mataimakin Gwamna da kuma SSG, inda ya ce Kwamishinan ‘Yan Sandan ya fusata bayan wasu mahalarta taron sun yi masa ihu yayin da yake kan mumbari.
A cewarsa, bayan komawar Gotan kujerarsa, sai ya lura cewa SSG ya yi dariya, lamarin da ya sa Kwamishinan ya ɗauki waya ya yi wasu kira.
Egbedun ya ce ya yi hasashen cewa an ba da umarnin kama SSG, kuma bayan ƴan mintuna kaɗan aka kira Igbalaye aka sanar da shi cewa jami’an ‘yan sanda na jiransa a gidansa.
Bayan haka, SSG ya shaida masa cewa an gayyace shi zuwa Sashen Binciken Laifuka (CID), inda aka ce an gano kuɗi da katunan zaɓe biyu a harabarsa.
Sai dai rundunar ‘yan sandan Osun ta bayyana cewa jami’anta sun kai samamen ne bisa sahihan bayanan sirri kan wasu da ake zargin masu laifi ne, inda suka kama mutane shida tare da kwato Naira miliyan 4.81, katunan zaɓe biyu, rajistar masu kaɗa ƙuri’a da wasu kayayyaki da ake zargin suna da alaƙa da laifukan zaɓe.
Egbedun ya kuma yi zargin cewa Kwamishinan ‘Yan Sandan ya taɓa ƙoƙarin tsorata shi, yana mai cewa ya taba umartar a janye jami’an tsaron da ke tare da shi duk da barazanar da yake fuskanta daga wasu ƴan daba.
Ya ce har yanzu yana samun rahotannin cewa ana ƙoƙarin ƙirƙiro masa laifi domin kama shi, amma ya jaddada cewa ba zai bar Jihar Osun ko gidansa ba saboda tsoro.
A ƙarshe, Kakakin Majalisar ya yi kira ga Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Olatunji Disu, da ya shiga cikin lamarin tare da binciken zarge-zargen da ake yi kan Kwamishinan ‘Yan Sandan Osun, domin tabbatar da adalci da kare haƙƙin jama’a
