Rikicin da ke addabar Majalisar Dokokin Jihar Ondo ya sake ɗaukar sabon salo, bayan wasu ‘yan majalisa sun zargi Gwamna Lucky Aiyedatiwa da hana aiwatar da shirin tsige Kakakin Majalisar, Olamide Oladiji.
Rahotanni sun ce ‘yan majalisa 21 cikin 26 sun rattaba hannu kan takardar tsige kakakin, bisa zargin karkatar da Naira miliyan 44 da aka ware domin sake tsara kasafin kuɗin Hukumar Raya Yankunan Masu Arzikin Mai ta Jihar Ondo.
Sai dai Kakakin Majalisar ya musanta zarge-zargen, yana mai cewa babu gaskiya a cikinsu.
Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai na Majalisar, Olatunji Fabiyi, ya ce an sake bai wa Kakakin wa’adin kwana bakwai, wanda zai ƙare a ranar Lahadi mai zuwa, kafin a ɗauki matakin tsige shi idan bai sauka daga mukaminsa ba.
Fabiyi ya kuma yi zargin cewa Gwamna Aiyedatiwa na tuntuɓar wasu ‘yan majalisar domin su janye goyon bayansu ga shirin tsige Kakakin.
Ya buƙaci gwamnan da ya bar majalisar ta gudanar da harkokinta ba tare da tsoma bakin ɓangaren zartarwa ba, yana mai cewa batun shugabancin majalisa hakki ne na ‘yan majalisar.
Sai dai a martaninsa, Mai Magana da Yawun Gwamnan, Ebenezer Adeniyan, ya musanta zargin, yana cewa Gwamna Aiyedatiwa bai tsoma baki a harkokin Majalisar ba, kuma abin da ya fi ba shi muhimmanci shi ne tabbatar da zaman lafiya, doka da oda a jihar.
