Ɗan wasan baya na Arsenal, Jurrien Timber, ya bar sansanin atisayen ƙungiyar da ke ƙasar Spain na ɗan lokaci, inda ya koma Landan domin ci gaba da jinyar raunin da ya samu a maraina (groin).
Rahotanni sun bayyana cewa komawar Timber ba saboda sabon rauni ba ne, sai dai wani ɓangare ne na tsarin jinyarsa da ƙungiyar ta tsara tun farko.
Ana sa ran ɗan wasan mai shekaru 24 zai koma Spain domin sake haɗuwa da tawagar koci Mikel Arteta bayan kammala wannan mataki na jinyar.
Timber na fama da raunin maraina bayan ya murmure daga raunin idon sawu da ya samu a ƙarshen kakar wasan da ta gabata, kuma Arsenal na ci gaba da sa ido kan lafiyarsa kafin fara sabuwar kakar wasa.
