Kamfanin Oando Energy Resources ya bayyana shirinsa na fara wani gwaji na samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da tsoffin rijiyoyin mai da aka daina amfani da su, a wani sabon yunƙuri na inganta samar da makamashi a Najeriya.
An bayyana hakan ne yayin wata ziyara da shugabannin kamfanin suka kai wa Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, inda suka tattauna kan gudummawar Oando ga fannin wutar lantarki da kuma muhimmancin amfani da iskar gas da ake samarwa a cikin gida.
Manajan Daraktan Oando Energy Resources, Dr. Ainojie Irune, ya ce aikin gwajin zai mayar da tsoffin rijiyoyin mai da ke ƙarƙashin haɗin gwiwar Oando zuwa hanyoyin samar da wutar lantarki irin ta geothermal.
Ya bayyana shirin a matsayin ɗaya daga cikin sabbin hanyoyin da ‘yan Najeriya suka kirkira domin magance matsalolin makamashi da kuma faɗaɗa samar da wutar lantarki a ƙasar.
Irune ya ce aikin na cikin dabarun Oando Clean Energy, wani shiri da kamfanin ya kafa shekaru biyar da suka gabata domin haɗa amfani da iskar gas, hasken rana, iska da ruwa wajen samar da ingantacciyar wutar lantarki mai araha ga ƙasashen Afirka.
Ya kuma bayyana cewa Oando na taka muhimmiyar rawa wajen samar da wutar lantarki ta hanyar tashar Okpai Independent Power Plant mai ƙarfin megawatt 480, wadda ke ciyar da wutar lantarki kai tsaye zuwa babban layin wutar lantarki na ƙasa.
A cewarsa, tashar na samar da wutar lantarki ga kusan ‘yan Najeriya miliyan 50, kuma tana bayar da kusan kashi 15 cikin 100 na jimillar wutar lantarkin ƙasar.
Irune ya ƙara da cewa kamfanin na ci gaba da karkata jarinsa zuwa fannin iskar gas, yana mai cewa bunƙasa amfani da iskar gas a cikin gida yana da matuƙar muhimmanci wajen farfaɗo da tattalin arziki da bunƙasa masana’antu.
A nasa jawabin, Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ya yaba da ƙoƙarin Oando, yana mai jaddada cewa Gwamnatin Tarayya na ci gaba da ba da fifiko ga amfani da iskar gas, wutar lantarki daga ruwa da hasken rana domin bunƙasa masana’antu da samar da isasshen wutar lantarki.
Ministan ya kuma yi maraba da tayin Oando na ba da tallafin fasaha da shawarwari, yana mai cewa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu zai taimaka wajen aiwatar da sauye-sauye masu ɗorewa a fannin wutar lantarki.
Bangarorin biyu sun amince da ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa a makonni masu zuwa domin cimma burin sauya fasalin fannin makamashi a Najeriya.