Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta kai ziyarar girmamawa ga Sarkin Musulmi, Mai Alfarma Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, a Fadar Sarkin Musulmi da ke Sokoto, a wani ɓangare na ƙoƙarin inganta zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban ƙasa.
Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmad Aliyu, ya tarbi Uwargidan Shugaban Ƙasar tare da bayyana ziyarar a matsayin alamar kyakkyawar alaƙa tsakanin Fadar Shugaban Ƙasa, Masarautar Sarkin Musulmi da al’ummar Jihar Sokoto.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, gwamnan ya ce ganawar ta nuna muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin cibiyoyin gargajiya da gwamnati wajen magance ƙalubalen da ƙasa ke fuskanta da kuma inganta rayuwar al’umma.
Ya yabawa Oluremi Tinubu bisa ƙoƙarinta na tallafawa ‘yan Najeriya ta hanyar shirin Renewed Hope Initiative, yana mai cewa ayyukanta na jin ƙai suna taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban ƙasa.
Gwamna Ahmad Aliyu ya ce ziyarar ta ƙara tabbatar da kyakkyawar haɗin gwiwa tsakanin Fadar Shugaban Ƙasa, Gwamnatin Jihar Sokoto da Masarautar Sarkin Musulmi wajen bunƙasa zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba.
A ƙarshe, ya yi addu’ar Allah Ya ƙara wa Sarkin Musulmi lafiya da hikima, tare da yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Uwargidansa fatan samun nasara a jagorancin ƙasa.
