Shugaban ƙasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya ƙaddamar da sabuwar jam’iyyar siyasa mai suna Kiiraay, a wani mataki da ke ƙara nuna rarrabuwar kawuna tsakaninsa da tsohon Firaminista kuma tsohon abokinsa na siyasa, Ousmane Sonko.
Faye da Sonko sun hau mulki ne bayan yaƙin neman zaɓe da suka yi bisa alƙawarin kawo sauyi, bunƙasa tattalin arziki, tabbatar da adalci da kuma yaƙi da cin hanci da rashawa. Sai dai dangantakarsu ta lalace sakamakon saɓanin ra’ayi kan yadda za a tafiyar da gwamnati da kuma warware matsalolin tattalin arzikin ƙasar.
Wasu daga cikin magoya bayan Faye sun bayyana cewa suna ganin sabon shugaban ƙasar mutum ne mai son zaman lafiya, kuma suna fatan kafa sabuwar jam’iyyar zai ba shi damar aiwatar da manufofinsa ba tare da sabani a cikin gwamnati ba.
Wani masanin tattalin arziki daga Dakar, Ibra Faye, ya ce yana fatan shugaban ƙasar zai samu damar aiwatar da sauye-sauyen da ya yi alƙawari da su, yana mai cewa rikice-rikicen cikin jam’iyya sun hana hakan a baya.
A wajen taron ƙaddamar da jam’iyyar, Faye ya bayyana cewa Kiiraay ita ce babbar jam’iyya mafi ƙarfi a Senegal, yana mai nuna cewa magoya baya da dama, ciki har da shugabannin ƙananan hukumomi da wasu manyan jiga-jigan siyasa, sun shiga cikinta.
Sai dai jam’iyyar Pastef, wadda Sonko ke jagoranta, ta yi watsi da wannan ikirari, tana mai cewa duk da ficewar wasu fitattun mambobi, har yanzu tana samun sabbin mambobi da yawa.
Rahotanni sun nuna cewa Faye ya samu shugabancin ƙasar ne da babban goyon bayan Sonko, wanda aka hana tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2024 saboda hukuncin da kotu ta yanke a kansa kan batun ɓata suna.
Bayan rikicin da ya shiga tsakaninsu, Faye ya sallami Sonko daga mukamin Firaminista a ranar 22 ga Mayu, lamarin da ya sa magoya bayansa suka zaɓe shi a matsayin Kakakin Majalisar Dokokin Senegal.
Duk da hakan, Sonko na ci gaba da kasancewa shugaban jam’iyyar Pastef, wadda ke da rinjaye a majalisar dokokin ƙasar da kujeru 130 cikin 165.
A ƙarshen watan Yuni, Majalisar Dokokin Senegal ta amince da dokar rage wasu daga cikin ikon shugaban ƙasa, ciki har da hana shugaban ƙasa jagorantar jam’iyya ko haɗakar jam’iyyu. Sai dai daga baya Kotun Tsarin Mulki ta soke wannan tanadi.
