Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya bukaci a kara karfafa hadin gwiwa tsakanin Najeriya da kasar Switzerland domin bunkasa ci gaban kasa.
Obi ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da Jakadan Switzerland a Najeriya, Patrick Egloff, inda ya ce sun tattauna kan hanyoyin inganta ilimi, lafiya da rage talauci a matsayin muhimman ginshikan ci gaban kasa.
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya yaba da irin gudummawar da Switzerland ke bayarwa Najeriya, musamman a yankin Arewa maso Gabas, inda ya ce taimakon ya taimaka wajen bunkasa tattalin arziki, ayyukan jin kai da zaman lafiya.
Obi ya jaddada cewa gina hadin gwiwa bisa amincewa da manufofin ci gaban al’umma zai taimaka wajen samar da Najeriya mai ci gaba da wadata ga kowa.
