Gwamnatin Tarayya tare da CBN da NDIC sun bukaci a kara karfafa hadin gwiwa tsakanin hukumomin kula da bankuna da inshorar ajiya a kasashen Afirka domin tunkarar sabbin barazanar da fasahar zamani, AI da harkokin banki na kasashe daban-daban ke haifarwa.
An bayyana hakan ne a taron shekara-shekara na International Association of Deposit Insurers (IADI) Africa Regional Committee da aka gudanar a Abuja.
Shugaban NDIC, Thompson Oludare Sunday, ya ce wayar da kan jama’a da kuma shirin tunkarar matsalolin kudi suna da matukar muhimmanci wajen tabbatar da kwanciyar hankali a tsarin banki, yana mai gargadin cewa yada bayanan karya na iya haddasa fargaba cikin gaggawa.
Shi ma Ministan Kudi kuma Mai Kula da Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele, ya ce babu ci gaban tattalin arziki idan babu kwanciyar hankali a tsarin banki, yana mai jaddada cewa amincewar jama’a ga cibiyoyin kudi ita ce ginshikin ci gaban kasa.
A nasa bangaren, CBN ya bayyana cewa sake kara jarin bankuna da sauran gyare-gyaren da ake aiwatarwa za su taimaka wajen kare tsarin banki, karfafa tattalin arziki da kuma tabbatar da dorewar amincewar masu ajiya.