Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya amince da aikin gina gidaje 40 na alfarma (duplexes) ga alƙalan jihar kan kuɗi Naira biliyan 25 domin inganta walwala da yanayin zamansu.
Haka kuma, gwamnatin ta amince da ware Naira biliyan 1.9 domin kafa cibiyoyin jarrabawar Computer-Based Test (CBT) guda huɗu a yankin Orlu, tare da ƙaddamar da tsarin allunan talla na zamani (Smart Digital Signage) domin bunƙasa fasahar zamani a jihar.
Kwamishinan Yaɗa Labarai, Wayar da Kai da Dabaru, Declan Emelumba, ne ya sanar da hakan bayan taron Majalisar Zartarwar Jihar da gwamna ya jagoranta a Owerri.
A cewarsa, gidajen alƙalan za su ƙunshi wuraren shakatawa da sauran kayayyakin more rayuwa domin samar da ingantaccen muhalli ga jami’an shari’a.
Majalisar ta kuma amince da sakin Naira miliyan 900 nan take domin fara aikin cibiyoyin CBT guda biyu a Bishop Shanahan Okoye Secondary School da Community Secondary School, Omuma.
Bugu da ƙari, gwamnatin ta amince da kafa Imo Signage Asset Management Limited, kamfani da zai kula da tsarin allunan talla na zamani ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu (PPP).
Kwamishinan Tattalin Arzikin Zamani da Gwamnatin Intanet, Chimezie Amadi, ya bayyana cewa aikin tsarin allunan talla zai gudana ne ba tare da gwamnatin jihar ta kashe kuɗi ba, domin masu zuba jari ne za su ɗauki nauyin aiwatar da shi.
