Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta taya sabuwar shugabar Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA), Misin Badejo-Okusanya (SAN), murnar nasarar da ta samu a zaɓen shugaban ƙungiyar.
Natasha ta bayyana cewa wannan nasara ba wai ta Misis Badejo-Okusanya kaɗai ba ce, har ma babbar nasara ce ga fannin shari’a da kuma Najeriya baki ɗaya. Ta ce hakan ya nuna cewa ƙwarewa, jajircewa da nagarta na iya kai mutum ga kololuwar jagoranci.
Ta ƙara da cewa zaɓen ya zama babban abin ƙarfafawa ga mata da ‘yan mata a Najeriya, domin yana nuna cewa mata ma za su iya kaiwa manyan muƙaman jagoranci.
A zaɓen da aka gudanar, Misin Badejo-Okusanya ta samu ƙuri’u 12,317, inda ta doke Lateef Akangbe (SAN) da ya samu 7,934, yayin da Aare Olumuyiwa Akinboro (SAN) ya samu 5,855.
Da wannan nasara, ta zama shugaba ta 33 ta NBA, kuma mace ta biyu da za ta jagoranci ƙungiyar, sannan ita ce mace ta farko da aka zaɓa kai tsaye ta hanyar zaɓe domin jagorantar NBA. Za ta yi wa’adin mulki daga 2026 zuwa 2028.
