Gwamnan Jihar Filato, Barr. Caleb Mutfwang, ya bayyana cewa aikin faɗaɗa da gina titin Maraban Jama’a–Pankshin–Langtang–Shendam–River Ibi zai kasance muhimmin ci gaba da zai buɗe sabbin damar bunƙasa tattalin arzikin jihar da ma yankin Arewa ta Tsakiya.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Harkokin Jama’a na gwamnan, Dr. Gyang Bere, ya fitar, Mutfwang ya ce amincewar gwamnatin tarayya da wannan babban aikin hanya na nuna kudirin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na rage gibin ababen more rayuwa da kuma tabbatar da ci gaban ƙasa baki ɗaya.
Gwamnan ya ce titin zai sauƙaƙa zirga-zirgar mutane da kayayyaki, rage kuɗin sufuri, ƙarfafa noma da kasuwanci, jawo masu zuba jari, bunƙasa yawon buɗe ido tare da inganta hulɗar tattalin arziki tsakanin jihohin Filato da Taraba da sauran yankuna.
A cewarsa, aikin ba gina hanya kaɗai ba ne, har ila yau zai samar da ayyukan yi, buɗe ƙauyuka ga ci gaba, da kuma ƙarfafa tattalin arzikin yankunan Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Gabas.
Mutfwang ya miƙa godiyarsa ga Shugaba Tinubu bisa amincewa da aikin, yana mai cewa hakan ya nuna gwamnatin tarayya tana sauraron buƙatun al’ummar Filato tare da ɗaukar matakan da suka dace.
Haka kuma ya yaba wa Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, saboda ƙoƙarinsa na isar da muradun al’ummar Filato ga shugaban ƙasa, tare da gode wa Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, kan jagorancin aiwatar da ayyukan ababen more rayuwa a ƙarƙashin shirin Renewed Hope.
Gwamnan ya yi kira ga al’ummar jihar Filato da su ci gaba da haɗin kai ba tare da la’akari da bambancin siyasa, ƙabila ko addini ba, domin samun ƙarin ayyukan ci gaba daga gwamnatin tarayya.
Ya kuma bayyana cewa idan aka kammala aikin titin, zai kasance ɗaya daga cikin manyan ayyukan raya yankin, wanda al’ummar Filato da Taraba za su ci gaba da tunawa da shi na tsawon lokaci.
