Gabanin zaɓen shekarar 2027, mutum shida daga cikin mutum 11 da suka nemi tikitin takarar gwamnan Jihar Oyo a jam’iyyar APC sun bayyana cewa ba su amince da Sanata Sharafadeen Alli a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar ba.
Waɗanda suka nuna rashin amincewar sun haɗa da Injiniya Hakeem Alao, Injiniya Rauf Olaniyan, Dr. Ayobami Lam-Adesina, Barista Akeem Agbaje, Ololade Bakare da Barista Musibau Asanike.
Sun ce jam’iyyar ba ta bi ƙa’idojin doka da tsarin cikin gida wajen zaɓen ɗan takarar ba, don haka a halin yanzu APC ba ta da sahihin ɗan takarar gwamna a jihar.
Sun bayyana matsayinsu ne bayan ganawa da kwamitin sulhu da jam’iyyar ta kafa ƙarƙashin jagorancin Sanata Olufemi Lanlehin da Farfesa Taoheed Adedoja domin sasanta rikicin da ya biyo bayan zaɓen fidda gwani.
Da yake magana a madadin sauran masu ƙorafin, Hakeem Alao ya ce sun bayyana dukkan korafe-korafensu ga kwamitin, yana mai jaddada cewa har yanzu ba a cika tanadin dokar zaɓe ba wajen ayyana ɗan takarar.
Sai dai ya ce duk da rikicin, suna fatan jam’iyyar za ta warware matsalar cikin gida, kuma duk wanda aka tabbatar da shi bisa doka a ƙarshe za su mara masa baya.
