Tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe na jam’iyyar SDP a zaɓen 2023, Kelmi Lazarus, ya fice daga jam’iyyarsa tare da komawa jam’iyyar PDP, inda ya bayyana goyon bayansa ga ɗan takarar gwamna na jam’iyyar, Farfesa Isa Ali Pantami.
Lazarus, wanda ya taɓa zama shugaban SDP na jihar da kuma Babban Manajan Radio Gombe, ya ce ya ɗauki wannan mataki ne bayan doguwar tattaunawa da masu goyon bayansa.
Ya bayyana cewa ya gamsu da cewa Pantami yana da hangen nesa, ƙwarewa, nagarta da kuma ƙwarewar shugabanci da za su iya kawo ci gaba mai ma’ana ga Jihar Gombe.
A cewarsa, Pantami shi ne ɗan takarar da ya fi dacewa da jagorantar jihar, tare da kira ga al’ummar Gombe da su mara wa PDP baya domin samun ci gaba da bunƙasar jihar.
A martaninta, jam’iyyar PDP reshen Jihar Gombe ta bayyana komawar Lazarus a matsayin babban ƙarfi ga jam’iyyar, tana mai cewa hakan na nuna ƙarin amincewar shugabanni da masu ruwa da tsaki ga manufofin jam’iyyar da kuma jagorancin Farfesa Isa Ali Pantami.
Jam’iyyar ta yi maraba da Lazarus da magoya bayansa, tare da tabbatar musu da cikakken damar ba da gudummawa wajen gina Jihar Gombe mai haɗin kai, zaman lafiya da ci gaba.
