Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, a ranar Laraba ya kai ziyara yankin Ogombo da ke ƙaramar hukumar Eti-Osa domin duba irin barnar da ambaliyar ruwa ta yi tare da ganawa da mazauna yankin da abin ya shafa.
Gwamnan ya samu rakiyar Mataimakin Gwamna, Obafemi Hamzat, Kwamishinan Muhalli da Albarkatun Ruwa, Tokunbo Wahab, da sauran manyan jami’an gwamnatin jihar.
Baya ga Ogombo, tawagar ta kuma kai ziyara yankunan Monastery Road–Sangotedo, Gbetu, Iwerekun da wasu yankuna da ke ƙarƙashin Eti-Osa East LCDA, domin tantance halin da ake ciki bayan mamakon ruwan sama.
Hotunan bidiyo da aka wallafa sun nuna Sanwo-Olu da tawagarsa suna ratsawa cikin ruwan ambaliya mai zurfin gwiwa yayin da suke duba lalacewar da ta faru tare da tattaunawa da mazauna yankunan.
Ziyarar na daga cikin matakan gwamnatin jihar na tantance barnar ambaliya da kuma ƙara inganta hanyoyin magance irin wannan matsala a yankunan da abin ya fi shafa.
