Gwamnatin Jihar Oyo ta musanta rahotannin da ke cewa ta biya kudin fansa domin ganin an sako dalibai da malamai da ‘yan bindiga suka sace a karamar hukumar Oriire, tana mai bayyana rahotannin a matsayin karya da yaudara.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Dotun Oyelade, ya sanya wa hannu a ranar Juma’a, gwamnatin ta ce ikirarin ba shi da tushe kuma wasu marasa kishin kasa ne ke yada shi domin rikitar da jama’a.
Sanarwar ta ce duk da kokarin hadin gwiwa da gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro ke yi domin ceto daliban da malaman cikin koshin lafiya, ba a biya kudin fansa ga ‘yan bindiga ba, kai tsaye ko a kaikaice.
Gwamnatin ta bukaci jama’a da su yi watsi da irin wadannan rahotanni tare da dogaro da bayanan da hukumomin gwamnati ke fitarwa kawai.
Oyelade ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar na ci gaba da aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro domin tabbatar da an kubutar da wadanda aka sace cikin aminci tare da kawo karshen wannan lamari.
A ranar 15 ga Mayu, 2026, wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan makarantu uku da ke Yawota da Ahoro-Esienle a karamar hukumar Oriire, inda suka sace dalibai da malamai tare da kashe wani malami yayin harin.
Har yanzu wadanda aka sace suna hannun masu garkuwa da mutanen, yayin da gwamnatin jihar, gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro ke ci gaba da kokarin ganin an ceto su lafiya.
