Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya bayyana cewa Najeriya ta gaza bayyana kashe kudaden gwamnati da suka kai kimanin Naira tiriliyan 8.83, wanda ya yi daidai da kusan dala biliyan 6.15, a cikin kasafin kudin gwamnati na baya-bayan nan.
Wakilin IMF a Najeriya, Christian Ebeke, ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da shugabannin kamfanoni a Legas ranar Laraba.
A cewarsa, wannan adadi wanda ya kai kashi biyu cikin dari (2%) na GDP, ya haifar da bambanci tsakanin gibin kasafin kudin da gwamnati ke bayyana da kuma hakikanin bukatar kudin da take aro domin gudanar da ayyukanta.
Rahoton ya nuna cewa an yi wannan lissafi ne bisa sabon alkaluman Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS), wadda ta bayyana cewa darajar tattalin arzikin Najeriya (Nominal GDP) ta kai Naira tiriliyan 441.5 a shekarar 2025, daga Naira tiriliyan 372.8 a shekarar 2024.
Ebeke ya ce wasu manyan ayyukan raya kasa da gwamnatin ke aiwatarwa ba a rubuta su cikin kasafin kudi ko rahotannin aiwatar da kasafin ba, lamarin da ya sa gibin kasafin kudi ya bayyana ƙasa da yadda yake a zahiri.
Ya bukaci a rika rubuta da kuma bayyana dukkan irin wadannan kashe-kashe domin a samu cikakken bayani kan yadda ake tafiyar da kudaden gwamnati.
Rahoton ya zo ne bayan NBS ta sake sabunta tsarin lissafin GDP ta hanyar sauya shekarar tushe daga 2010 zuwa 2019, matakin da ya kara girman darajar tattalin arzikin Najeriya da kuma darajar kudaden da ake lissafawa bisa kaso na GDP.
