Gwamnatin Jihar Kebbi ta musanta rahotannin da ke ikirarin cewa wata sabuwar kungiyar ta’addanci mai suna “Sai Malam” ta bayyana a jihar.
Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu na jihar, Alhaji Yakubu Ahmed, ya bayyana cewa rahoton karya ne da aka kirkira domin yaudarar jama’a gabanin zaben shekarar 2027.
Ahmed ya ce binciken da Hukumar Tsaro ta DSS da rundunar ‘yan sanda suka gudanar ya nuna cewa mutanen da ake kira “Sai Malam” ba kungiyar ta’addanci ba ce, illa wasu matasa da ke aikata damfara ta yanar gizo da kuma karbar kudi ta hanyar yaudara.
Ya kara da cewa an riga an kama wasu daga cikinsu, kuma su ne ake kira ‘Yan Vocal, wadanda ake kuskuren danganta su da kungiyar “Sai Malam”.
Har ila yau, kwamishinan ya karyata rahoton da ya ce yara sama da 130 na mutuwa a kullum a jihar Kebbi, yana mai cewa wannan ikirari ba gaskiya ba ne, kuma UNICEF ta tabbatar wa gwamnatin jihar cewa ba ita ce ta fitar da irin wannan rahoto ba.
A nasa bangaren, Manajan Daraktan Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN), Malam Ali M. Ali, ya ce yawaitar amfani da kafafen sada zumunta da fasahar AI na taimakawa wajen yada labaran karya, inda ya bukaci masu yada bayanan gwamnati su kasance masu gaggawar fitar da sahihan bayanai domin dakile jita-jita.
