Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta fuskanci suka da martani mabambanta a kafafen sada zumunta bayan ta bukaci ‘yan Najeriya su rungumi ƙananan sana’o’i kamar sayar da ƙosai, gasasshen masara da ƙuli-ƙuli domin samun abin dogaro.
Da take zantawa da wakilan fadar shugaban ƙasa bayan taron kwata na biyu na shirin Renewed Hope Initiative (RHI) tare da matan gwamnoni a Abuja, Remi Tinubu ta ce irin waɗannan sana’o’i ba sa buƙatar kuɗi masu yawa kafin a fara su.
Ta bayyana cewa masu cin gajiyar shirin ba rance ake ba su ba, sai dai tallafin kuɗi (grant) domin su kafa sana’o’insu da inganta rayuwarsu.
Ta ce, “Muna ƙoƙarin ba mutane fata. Fara sana’ar ƙosai ba ya buƙatar kuɗi masu yawa. Haka ma gasasshen masara ko ƙuli-ƙuli. Ba rance muka ba su ba, tallafi muka ba su.”
Uwargidan shugaban ƙasar ta kuma bayyana wasu ayyukan da shirin Renewed Hope Initiative ya aiwatar, ciki har da tallafa wa bangaren lafiya, noma, ilimi da shirye-shiryen inganta rayuwar al’umma.
A cewarta, ta bayar da gudummawar Naira biliyan biyu domin yaƙi da cutar tarin fuka (tuberculosis), Naira biliyan ɗaya don tallafawa masu fama da cutar sankarar mama, sannan Naira miliyan 500 domin yaƙi da matsalar tamowa a faɗin ƙasar.
Har ila yau, ta ce shirin ya samar da guraben karatu, horaswar fasahar sadarwa (ICT) da tallafin noma domin ƙarfafa marasa galihu.
Remi Tinubu ta buƙaci ‘yan Najeriya kada su yanke ƙauna duk da matsin tattalin arzikin da ake fuskanta, tana mai cewa manufar Renewed Hope Agenda ita ce samar da fata da inganta rayuwar talakawa.
Sai dai kalamanta sun haifar da muhawara a kafafen sada zumunta. Wasu sun soki furucin nata, suna masu cewa ya nuna rashin fahimtar irin wahalhalun tattalin arzikin da jama’a ke ciki, inda suka ce abin da ‘yan Najeriya ke buƙata shi ne samar da ayyukan yi, rage tsadar rayuwa da bunƙasa tattalin arziki.
A gefe guda kuma, wasu sun kare Uwargidan Shugaban Ƙasar, suna cewa babu aibu a kowace irin halalacciyar sana’a, kuma sana’o’in ƙosai, gasasshen masara da ƙuli-ƙuli sun daɗe suna tallafawa dubban iyalai a Najeriya.
