Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa National Health Technology and Data Analytics Office (NHTDAO) domin jagorantar daidaitawa da bunƙasa tsarin kiwon lafiya na zamani da amfani da bayanai a Najeriya.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Juma’a.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa Shugaban Ƙasar ya naɗa Dr. Obi Adigwe, Darakta Janar na National Institute for Pharmaceutical Research and Development (NIPRD), a matsayin Kodinetan na farko na sabuwar hukumar.
A cewar sanarwar, ofishin zai kasance ƙarƙashin Ofishin Ministan Kula da Lafiya da Jin Daɗin Jama’a, kuma zai jagoranci aiwatar da manufofin tsarin kiwon lafiya na dijital a ƙasar.
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa sabuwar hukumar ba za ta maye gurbin ayyukan hukumomin lafiya da ke akwai ba, sai dai za ta haɗa kai da su tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin cibiyoyin gwamnati da masu zaman kansu.
Hukumar za ta kuma samar da ƙa’idoji da tsarin haɗa bayanan lafiya a faɗin ƙasar, tare da aiwatar da National Digital Health Architecture, wanda Majalisar Kula da Lafiya ta Ƙasa ta amince da shi tun a watan Nuwamban 2025.
Sanarwar ta ƙara da cewa za a riƙa gudanar da aikin hukumar ƙarƙashin wani kwamitin jagoranci wanda Ministan Kula da Lafiya da Jin Daɗin Jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate, da Shugaban Nigerian Economic Summit Group (NESG), Olaniyi Yusuf, za su jagoranta tare.
Fadar Shugaban Ƙasa ta ce ana sa ran sabuwar hukumar za ta hanzarta sauya tsarin kiwon lafiya na Najeriya zuwa tsarin zamani mai amfani da fasahar dijital, wanda zai kasance mai tsaro, haɗa bayanai cikin sauƙi, da kuma inganta ayyukan kiwon lafiya ga dukkan ‘yan ƙasa, daidai da manufar Renewed Hope Agenda ta gwamnatin Tinubu.
