Mahukuntan Jami’ar Jihar Rivers (Rivers State University) sun haramta wa ɗaliban digirin farko tuka motocinsu cikin harabar jami’ar daga karfe 4:00 na yamma zuwa 7:00 na safe, bayan mutuwar wata ɗaliba mai shekaru 21 da wata mota ta buge.
Mukaddashin Magatakardar jami’ar, Dr. Idanyingi Daminabo, ya sanar da matakin yayin ganawa da manema labarai a Port Harcourt ranar Juma’a.
Ya ce an ɗauki wannan mataki ne bayan rasuwar Eno Udoson, wadda aka ce wata mota da wani ɗalibi ke tukawa cikin gudun wuce kima ta buge a harabar jami’ar ranar Talata.
Daminabo ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamaciyar, abokanta da sauran ɗaliban jami’ar.
Ya bayyana cewa binciken farko ya nuna hatsarin ya shafi ɗalibai biyu, Darlington Onuaku na Sashen Development and Communication Studies da Obinna Ikechi na Sashen Computer Science.
A cewarsa, an kama ɗaliban biyu kuma an miƙa su hannun ‘yan sanda domin ci gaba da bincike da yiwuwar gurfanar da su a kotu.
Ya ce jami’ar ta riga ta kafa dokar takaita gudun mota, sanya kwantar da gudu da kuma hukunta masu karya dokokin tuki, amma bayan taron gaggawa da mahukunta suka yi, an ƙara wasu sabbin matakan tsaro.
Sabbin dokokin sun haɗa da haramta wa ɗaliban digirin farko shigo da motocinsu cikin harabar jami’a tsakanin ƙarfe 4:00 na yamma zuwa 7:00 na safe.
Haka kuma, duk ɗalibin da ya zo da mota zai ajiye ta ne a filin ajiye motoci da ke kusa da babbar ƙofar jami’ar, sannan ya yi amfani da motocin sufuri da jami’ar ta amince da su wajen zirga-zirga a cikin harabar makarantar.
Jami’ar ta kuma bayyana cewa ɗaliban digiri na biyu da masu karatu a Centre for Continuing Education za a ba su damar shiga da motocinsu ne kawai idan sun gabatar da ingantacciyar katin shaidar jami’a.
Daminabo ya yi gargaɗin cewa duk ɗalibin da aka kama da tuki cikin ganganci zai fuskanci dakatarwa daga karatu, matakin ladabtarwa da kuma ƙwace motarsa.
Ya ƙara da cewa lokutan ziyartar ɗakunan kwanan ɗalibai yanzu za su ƙare da ƙarfe 6:00 na yamma, yayin da iyakar gudun mota ta ci gaba da kasancewa kilomita 30 a manyan tituna da kilomita 20 a yankunan zama.
A halin da ake ciki, Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Rivers ta tabbatar da kama mutane biyu dangane da mutuwar ɗalibar, inda ta ce bincike na ci gaba kuma duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukuncin doka.
Wani ɗan uwan mamaciyar kuma malami a jami’ar, Moore Mike-Ogburia, ya yi zargin cewa direbobi biyu ne ke tseren mota lokacin da suka yi karo, lamarin da ya jawo mutuwar Eno Udoson.
Ya buƙaci hukumomi su tabbatar da an hukunta waɗanda ke da alhakin lamarin, yana mai cewa tsaurara bin dokokin hanya tun da farko da ya hana irin wannan mummunan hatsari faruwa.
