Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, na shirin gabatar da bukatar cewa babu hujjar ci gaba da shari’ar da ake yi masa, bayan Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ta kammala gabatar da shaidunta a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
DSS na tuhumar El-Rufai ne da laifuka biyar da suka hada da zargin sauraren tattaunawar waya ba bisa ka’ida ba da kuma karya dokokin tsaron kasa.
A cewar takardun tuhumar, El-Rufai ya bayyana a wata hira da gidan talabijin na Arise TV a watan Fabrairun bana cewa ya samu damar sauraren wata tattaunawar waya da ta shafi mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.
An ce tsohon gwamnan ya yi ikirarin cewa tattaunawar ta bayyana wani shiri na jami’an tsaro na kama shi, lamarin da DSS ta ce ya saba wa sashe na 12(1) na dokar Cybercrimes (Amendment) Act ta shekarar 2024.
A zaman kotun na ranar Talata, lauyan DSS, Oluwole Aladedoye, ya sanar da kotun cewa masu gabatar da kara ba za su sake kiran wani shaida ba, inda suka rufe gabatar da shari’arsu.
Bayan wannan mataki, lauyan El-Rufai, Paul Erokoro (SAN), ya bayyana wa kotu cewa bangaren masu kare kansu za su shigar da bukatar no-case submission, wato neman kotu ta watsar da karar bisa hujjar cewa DSS ba ta gabatar da isassun hujjojin da za su tilasta wa wanda ake kara ya kare kansa ba.
Bangaren El-Rufai ya nemi makonni biyu domin gabatar da bukatar, yayin da masu gabatar da kara suka nemi karin makonni biyu domin mayar da martani.
Haka kuma, Erokoro ya bukaci kotu ta sassauta sharuddan belin da aka gindaya wa tsohon gwamnan, yana mai cewa sharuddan suna da tsauri kuma suna da wahalar cikawa.
Ya bayyana cewa sharadin samar da ma’aikatan gwamnati masu matsayi na Level 17 da ke da kadarori a yankunan Maitama ko Asokoro na Abuja, tare da wasu takardun tabbatarwa daga Majalisar Sarakunan Jihar Kaduna, ya yi tsauri matuka.
Sai dai DSS ta yi adawa da bukatar, tana mai cewa akwai ma’aikatan gwamnati da za su iya cika wadannan sharudda.
Da take yanke hukunci kan bukatar, Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta ki amincewa da sauya sharuddan belin, tana mai cewa akwai mutanen da za su iya zama masu tsaya masa kamar yadda kotu ta bukata.
Daga nan kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 22 ga Satumba domin sauraron bukatar no-case submission da kuma ci gaba da shari’ar.
