Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya amince da nadin Terry Igiebor a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Asusun Muhalli da Gudanar da Harkokin Muhalli ta Jihar Edo.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Umar Ikhilor, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce nadin na daga cikin kokarin gwamnati na karfafa kula da muhalli da bunkasa ci gaban al’umma a matakin kasa.
An bayyana Igiebor a matsayin fitaccen dan kasuwa kuma gogaggen dan siyasa mai kusanci da jama’a, wanda ya yi fice wajen ayyukan ci gaban al’umma da tallafawa jama’a musamman a matakin karkara.
A baya, ya taba zama mamba a Hukumar Binciken Kudi ta Jihar Edo, inda ya taka rawa wajen bunkasa gaskiya, rikon amana da kyakkyawan shugabanci.
Sanarwar ta ce za a mika sunan Igiebor ga Majalisar Dokokin Jihar Edo domin yin nazari tare da tabbatar da nadin nasa kamar yadda doka ta tanada.
“Wannan sanarwa ce ta nadin Terry Igiebor a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Asusun Muhalli da Gudanar da Harkokin Muhalli ta Jihar Edo. Za a mika nadin ga Majalisar Dokokin Jihar Edo domin tantancewa da tabbatarwa bisa tanadin doka,” in ji sanarwar.
Ikhilor ya kara da cewa ana sa ran nadin zai taimaka wajen inganta yadda ake gudanar da kudaden muhalli tare da magance kalubalen da suka shafi muhalli a jihar.
Ya ce hakan zai kuma taimaka wajen aiwatar da shirye-shiryen ci gaba mai dorewa da gwamnatin jihar ke kokarin samarwa domin amfanin al’ummar Edo baki daya.
