Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yabawa rundunar sojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro bisa nasarar da suka samu a wani samame da ya kai ga kashe fitaccen shugaban ‘yan bindiga Ibrahim Bastuji a Jihar Kogi, tare da ceto Hajiya Amina Rabe Abubakar, matar marigayi tsohon Daraktan Yada Labaran Tsaro, Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya. Shugaban ya bayyana wannan nasara a matsayin babban koma baya ga kungiyoyin masu aikata laifuka da suka dade suna addabar al’ummomi a Kogi da jihohin makwabta, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta taba amincewa da mika ko da wani yanki na Najeriya ga ‘yan bindiga ko masu ta’addanci ba. Ya kuma tabbatar wa jami’an tsaro cikakken goyon bayan gwamnati domin kawo karshen matsalar rashin tsaro a fadin kasar nan.
Tinubu Ya Jinjinawa Sojoji Kan Kashe Dan Bindiga Ibrahim Bastuji Da Kuma Ceto Matar Marigayi Janar Rabe
Previous ArticleAPC Ta Ce Har Yanzu Pantami Mambanta Ne Duk Da Takararsa A PDP
Related Posts
Add A Comment
