Jam’iyyar APC reshen jihar Gombe ta bayyana cewa tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Farfesa Ali Pantami, har yanzu mamba ne na jam’iyyar saboda ba a bi ka’idojin ficewa daga jam’iyya yadda doka ta tanada ba.
Jam’iyyar ta ce kwamitin gudanarwa na APC a mazabar Pantami bai taba karbar ko tattauna wata takardar murabus daga gare shi ba, inda mafi yawan shugabannin mazabar suka bayyana batun ficewarsa a matsayin abin da ba su da masaniya a kai.
Sakataren Yada Labarai na APC a Gombe, Moses Kyari, ya ce bisa kundin tsarin mulkin jam’iyyar da dokokin zabe, Pantami zai ci gaba da kasancewa mamba a APC har sai an kammala dukkan matakan da suka dace na ficewa daga jam’iyyar.
Jam’iyyar ta kuma karyata ikirarin da ake cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da matakin Pantami na komawa PDP da kuma neman takarar gwamna a karkashin jam’iyyar adawa.
A cewar APC, Shugaba Tinubu mutum ne mai biyayya ga jam’iyyar kuma ba zai goyi bayan wani mataki da zai iya raunana hadin kan APC ba.
Jam’iyyar ta bukaci shugabancin APC na kasa da Fadar Shugaban Kasa su fito su yi karin haske kan lamarin domin kauce wa yada bayanan da ka iya rudar da jama’a.
Haka kuma ta sake jaddada kudirinta na tabbatar da gaskiya, hadin kai da kuma ci gaba da karfafa jam’iyyar a jihar 0Gombe.
