Babbar Kotun Tarayya ta Babban Birnin Tarayya (FCT) da ke zama a Maitama, Abuja, ta yi watsi da bukatar tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Adoza Bello, wadda ke neman a soke shari’ar zargin badakalar kudade ta Naira biliyan 110.4 da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ke yi masa.
Yahaya Bello na fuskantar shari’a tare da Umar Shuaibu Oricha da Abdulsalami Hudu kan tuhume-tuhume guda 16 da suka shafi karya amana da kuma halasta kudaden da ake zargin an samu ta haramtacciyar hanya.
A cikin bukatar da ya gabatar, Bello ya kalubalanci hurumin kotun FCT na sauraron karar, yana mai cewa akwai wata makamanciyar shari’a da ke gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Sai dai lauyan masu gabatar da kara, Kemi Pinheiro (SAN), ya bayyana cewa bukatar ba ta da tushe a shari’a, kuma an gabatar da ita ne domin jinkirta ci gaban shari’ar.
A hukuncin da Mai Shari’a Maryanne Anenih ta yanke, kotun ta amince da hujjojin masu gabatar da kara, inda ta tabbatar da cewa tana da hurumin sauraron karar. Ta kuma yi watsi da bukatar Yahaya Bello da wata irin ta wanda ake kara na uku, tana mai cewa dukkaninsu ba su da wani ingantaccen dalili.
Bayan yanke hukuncin, kotun ta umarci a ci gaba da sauraron karar, inda masu gabatar da kara suka gabatar da shaidu na 16 da na 17.
Shaidan farko, Baba Isah Usman Baffa, ya shaida wa kotu cewa Ali Bello ya sayi wani shago a Sherrif Plaza da ke Abuja kan Naira miliyan 66, inda aka biya Naira miliyan 40 da farko sannan aka kammala sauran kudin daga baya.
Shi kuwa shaidan na 17,shehu Bello, ya bayyana yadda ya taimaka wajen saye da sayar da kadarori daban-daban ga Ali Bello da wasu ‘yan uwansa a wurare kamar Guzape, Maitama da Wuse II a Abuja, inda ya bayyana darajar wasu kadarorin da suka kai daruruwan miliyoyin naira.
Daga bisani, Mai Shari’a Anenih ta dage sauraron karar zuwa ranar 17 ga Yuni, 2026 domin ci gaba da gabatar da shaidu da sauraron shari’ar.
