Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar Labour Party a zaɓen 2023, Peter Obi, wanda kuma ya ce ya lashe zaben fidda gwani na 2027 na National Democratic Congress (NDC), ya soki yadda gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke ci gaba da karɓar bashi, yana mai cewa ya yi yawa tare da ƙarancin bayani kan yadda ake amfani da kuɗaɗen jama’a.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafukan sa na sada zumunta a ranar Talata, Obi ya ce jimillar bashin Najeriya ya kai kusan Naira tiriliyan 200, wanda ya ce ya ƙaru da fiye da Naira tiriliyan 100 cikin shekaru uku.
Ya bayyana cewa wannan hauhawar bashi ya haifar da damuwa mai tsanani kan yadda ake tafiyar da tattalin arzikin ƙasa, musamman idan aka kwatanta da zamanin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, inda ya ce bashin ƙasar ya kai kusan Naira tiriliyan 49 bayan shekaru takwas a mulki.
Obi ya ce abin damuwa ba wai yawan bashin kaɗai ba ne, har ma da rashin isasshen bayani kan yadda ake amfani da kuɗaɗen da ake karɓa.
Ya ce bisa bayanan da ya ce ya samu daga Ofishin Kasafin Kuɗi na Tarayya, gwamnati ta karɓi bashi na Naira tiriliyan 11.89 a cikin watanni tara na farkon shekarar 2025, wanda ya wuce abin da aka tsara da kusan Naira tiriliyan 1.54.
Ya ƙara da cewa daga cikin kuɗaɗen da aka karɓa, Naira tiriliyan 3.10 ne kawai aka ware wa ayyukan raya ƙasa, wanda ya ce ya yi ƙasa da abin da ake buƙata.
Obi ya ce wannan ya haifar da giɓi mai yawa a aiwatar da ayyukan raya ƙasa, yana tambayar inda sauran kuɗaɗen suka tafi.
A cewarsa, gwamnati na da alhakin bayyana yadda take amfani da kuɗaɗen jama’a domin tabbatar da gaskiya da rikon amana.
Ya jaddada cewa bashi ya kamata ya haifar da ci gaban ƙasa mai ma’ana, ba kawai ƙara nauyin tattalin arziki ga al’umma ba.
