Tsohuwar Sanatar Ogun ta Tsakiya, Farfesa Iyabo Obasanjo, ta sanar da ficewarta daga jam’iyyar APC, tana mai zargin shugabannin jam’iyyar a Jihar Ogun da nuna mata rashin mutunci, wariya da kuma rashin adalci.
Iyabo, wacce ‘yar tsohon shugaban kasa ne, Cif Olusegun Obasanjo, ta bayyana hakan ne a cikin wasikar murabus da ta aikewa shugaban APC na jihar Ogun, Cif Yemi Sanusi, mai dauke da kwanan watan 31 ga Mayu.
Farfesar da ke koyar da ilimin annoba (Epidemiology) a Amurka ta soki tsarin da ya haifar da zaben Sanata Solomon Adeola, wanda aka fi sani da “Yayi”, a matsayin dan takarar gwamna na maslaha na jam’iyyar, tana mai cewa ba a bi ka’idojin APC ba.
Ta ce duk da cewa ta amince za ta goyi bayan duk wanda aka zaba ta hanyar maslaha, ba a tuntube ta ko saka ta cikin shirin da ya kai ga ayyana Adeola a matsayin dan takara ba.
Iyabo ta kuma yi zargin cewa an hana wasu daga cikin magoya bayanta shiga wurin da aka bayyana dan takarar, inda ta ce an yi musu barazana da tsoratarwa.
Duk da rashin jin dadinta, ta ce ta amince da sakamakon domin tabbatar da hadin kan jam’iyya, har ma ta taya Adeola murna a daren da aka ayyana shi a matsayin dan takarar maslaha.
Ta bayyana cewa daga baya Adeola ya nemi ganawa da magoya bayanta, inda aka gabatar masa da bukatu guda uku. A cewarta, ya yi alkawarin mayar da martani cikin mako guda, amma sama da watanni biyu kenan ba tare da ya yi hakan ba.
Iyabo ta ce wannan al’amari ya kara tabbatar mata da cewa ana raina gudunmawar da take bayarwa ga jam’iyyar.
“Idan abin da ake ci gaba da gabatar maka shi ne rashin mutunci, to lokaci ya yi da za ka tashi daga teburin. Saboda haka, na bar teburin APC inda ba a maraba da ni,” in ji ta.
Ta gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, shugaban APC na Ogun, Cif Yemi Sanusi, da shugabannin APC na Ogun ta Tsakiya bisa goyon baya da mutuncin da suka nuna mata yayin da take cikin jam’iyyar.
Iyabo Obasanjo ta koma siyasa a shekarar 2025 bayan ta yi rijista a matsayin mamba ta APC a gundumar Ibogun da ke karamar hukumar Ifo ta Jihar Ogun.
Ta taba zama Kwamishiniyar Lafiya ta Jihar Ogun tsakanin 2003 zuwa 2007, sannan ta wakilci Ogun ta Tsakiya a Majalisar Dattawa daga 2007 zuwa 2011.
Bayan rashin nasarar sake komawa Majalisar Dattawa a 2011, ta koma Amurka kuma ta yi nesa da siyasa har zuwa karshen shekarar 2025, lokacin da aka fara jin duriyarta ta neman kujerar gwamnan Ogun a karkashin APC kafin daga bisani ta fice daga jam’iyyar.
