Jam’iyyar Labour Party ta sanar da dage zaɓukan fidda gwani na shugaban ƙasa, gwamnoni, ‘yan majalisar tarayya da na jihohi zuwa ranar 30 ga watan Mayu, 2026.
Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Ken Asogwa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Alhamis.
Tun da farko, jam’iyyar ta tsara gudanar da zaɓen fidda gwani na gwamnoni da ‘yan majalisar jihohi a ranar 27 ga Mayu, yayin da na shugaban ƙasa da majalisar tarayya za su gudana a ranar 29 ga watan.
Sai dai Asogwa ya ce yanzu an haɗa dukkan zaɓukan domin a gudanar da su a rana guda, wato 30 ga watan Mayu.
A cewarsa, an ɗauki matakin ne saboda karo da jadawalin wasu muhimman bukukuwa da abubuwan ƙasa.
Ya ce, “Saboda muhimmancin bukukuwan Sallah da kuma bikin ranar 29 ga Mayu, jam’iyyar Labour Party ta ga dacewar sauya jadawalin domin bai wa mambobi, masu neman takara da sauran ‘yan Najeriya damar gudanar da waɗannan lokuta cikin kwanciyar hankali.”
Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa an ɗauki matakin ne domin nuna kulawa da haɗin kai, tare da neman afuwar duk wata matsala da sauyin jadawalin zai iya haifarwa ga masu ruwa da tsaki.
